Forex.market
Would you like to react to this message? Create an account in a few clicks or log in to continue.

Go down
avatar
Admin
Admin
Posts : 101
Join date : 2021-12-20
https://forex-market.africamotion.net

Wikifx:Kasan sanda zaka sayi ko ka sayar da jerin kudade. Empty Wikifx:Kasan sanda zaka sayi ko ka sayar da jerin kudade.

Fri Jan 14, 2022 11:29 pm
Kasuwar canjin kudi ta hada ne da has ashen wani kudi ne zaiyi daraja ko zai karye abisa wani kudin.

  Tayaya zaka san sanda zaka sayi kosayarda jerin kudade?

  A misalai masu zuwa, zamuyi amfani da a dan karamin muhimmin nazari dan ya taimaka mana wajen yanke hukuncin saye ko sayarda wani takamaiman jerin kudade biyu.

  Wadata da kuma bukatar kudade tana canjawa ne a sakamakon al’amuran tattalin arziki, wanda suke ingiza canjin farashin kudade zuwa sama da kasa.

  Wani kudi mallakin wata kasar ne (ko yanki). Saboda haka muhimman nazari na kasuwar canjin kudi yasa gaba ne wajen daukacin yanayin tattalin arzikin kasa, wanda ya hada da yawan (himmar) aiki, samar da aikin yi, samar da kayayyaki, kasuwancin kasa kasa, dakuma farashin riba.

  Farka daga bacci!

  Idan koda yaushe kana bacci ayayin gudanar ajinku na tattalin arziki ko kana guduwa daga ajin tattalin arziki, karka damu!

  Zamu tattauna dakyau akan muhimman nazarurruka a karatun gaba.

image_stage2.png
  Amma a yanzu, kayi kamar kasan abunda yake wakana…..

  EUR/USD

  A wannan misalin, euro shi ne kudi mai tushe saboda haka shi ne “tushen” saye da sayarwa.

  Idan kayadda cewa tattalin arzikin Amurca (U.S.) zai cigaba da yin rauni wanda abu ne mai muni gad alar Amurca, zaka zartar da umarni na siyan EUR/USD.

  Yin hakan yana nufin ka sayi euro da hasashen cewa zatayi daraja akan dalar Amurka (U.S).

  Idan ka yarda cewa tattalin arzikin Amurka (U.S.) yanada karfi sannan kuma euro zaiyi rauni akan dalar Amurka (U.S.), sai ka bada umarnin a siyar da EUR/USD.

  Yin hakan yana nufin ka sayar da euros da hasashen cewa zatayi rauni akan dalar Amurka (U.S.).

  USD/JPY

  a wannan misalign, dalar Amurca (U.S.) ita ce kudi mai tushe sannan kuma it ace “tushen” saye da sayarwa.

  Idan kana tunanin gwamnatin japan zata karya darajar kudinta (yen) domin ta taimakawa masana’antunta masu fitar da kaya kasashen waje, zaka bada umarnin a sayi USD/JPY.

  Ayayin da kayi haka, ka sayi dalar Amurka (U.S) da hasashen cewa zatayi daraja abisa kuydin Japan (yen).

  Idan kayi Imani cewa yan Japan da suka zuba jari suna janye kudadensu daga kasuwar kudin Amurca sannan suna juyar da gaba dayan dalar su ta Amurka (U.S.), to zaka bada umarnin a sayi USD/JPY.

  Yin hakan yana nufin ka sayar da dalar Amurka (U.S.) da has ashen cewa zata yi rauni akan kudin japan (yen).

  GBP/USD

  A wannan misalign fan shi ne kudin mai tushe saboda haka shi ne “tushen” saye da sayarwa.

  Idan kayi imani cewa tattalin arzikin Birtaniya (U.K) zai cigaba dayin kyau akan na Amurka (U.S) ta fannin habakar tattalin arziki, to zaka bada umarnin sayen GBP/USD.

  Ayayin da kayi haka, ka sayi fan da saran cewa zaiyi daraja fiyeda dalar amurca.

  Idan kayi imane cewa tattalin arzikin Birtaniya yana tafiyar hawainiya a yayin da na tattalin arzikin Amurka da karfi kamar Chuck Norris, tozaka bada umarnin a sayi GBP/USD.

  Ayayin da kayi haka, ka siyar da fan da has ashen cewa zai karye a daraja akan dalar Amurka.

  Yadda zakayi cinikayyar kasuwar canjin kudi da USD/CHF

  a wannan misalin, dalar Amurka (U.S.) Ita ce kudin tushe saboda haka ita ce tushen saye/sayarwa.

  Idan kana tunani cewa darajar kudin swiss (franc) ta wuce hankali, to sai bada umarnin siyan USD/CHF.

  A yayin da kayi haka, ka sayi dalar Amurka (U.S.) a has ashen cewa zatayi daraja akan kudin swiss (franc).

  Idan kayi Imani cewa raunin kasuwar amurka ta cikin gida zai cutarda habakar tattalin arziki anan gaba, wabda zai raunana dalar Amurka (U.S), zaka bada umarnin siyan USD/CHF.

  A yayin da kayi haka, to ka siyar da dalar Amurka (U.S.) da has ashen cewa darajarta zata fadi akan kudin swiss (franc).

  Cinikayya ta dandazo

  A yayin dakaje shagon sayarda kayayyaki zaka sayi kwai, baza ka iyan siyan kwai guda daya ba, saboda suna zuwa ne a shabiyu biyu ko da yawa.

  A kasuwar canjin kudi, zai zama shirme ne ka saya ko ka sayarda euro 1, saboda suna zuwa ne da yawa a adadin rabo 1,000 na kudi (dan kankanin yawa), a adadin rabo 10,000 (karamin yawa), ko kuma a adadin rabo 100,000 (kayyadadden yawa) ya danganta da dillalinka da kuma kalar asusun da kake dashi.

  Kasuwancin Jingina

  Saidai banida isasshen kudin dazan sayi euro 10,000! Shin duk da haka zan iya cinikayya?

  Kwarai zaka iya! Idan kayi amfani da jarin aro.

  Idan kayi cinikayya da jarin aro, baka bukatar sai ka biya euro 10,000 na somun tabi. A maimakon haka zaka saka yar karamar ajiyane wadda ake kira da jingina.

  Jarin aro shi ne kwatankwacin girman hadahada (“girman matsaya”) akan kudaden ainahi (“jarin cinikayya”) wanda ake amfani dasu a wajen jingina.

  Misali, 50:1 jarin aro, kuma an sanshi da 2% na abunda ake bukata domin yin jingina, wanda yake nufin $2,000 na jingina ake bukata domin abude matsaya mai girman data kai $100,000.

  Wannan shi ne yadda zaka iya bude matsaya ta $1,250 ko $50,000 alhali kana da dan kankanin kudin da bai wuce $25 ko $1,000 ba.

  Kasuwancin jingina yana baka dama ka bude matsaya mai girma alhali zakayi amfani ne kawai da dan bantare na jarin da dama zaka bukata.

  Wannan shi ne yadda zaka iya bude matsaya ta $1,250 ko $50,000 alhali kana da dan kankanin kudin da bai wuce $25 ko $1,000 ba.

  Zaka iya yin babbar mu’amala da dan kankani jarin farko.

  Bara muyi bayani.

  Zamu tattauna sosai akan jingina daga baya, amma muna fatan ka fuskanci muhimman abubuwa gameda da yadda take aiki.

  Kasaurara dakyau saboda wannan abu ne mai matukar muhimmanci.

  Kayi Imani cewa alama a kasuwa tana nuna fan din Birtaniya zaiyi daraja akan dalar Amurka.

  Kabude daidaitattaciyar cinikayya ta dandazo guda daya (100,000 units GBP/USD), siyayya da fan Birtaniya tareda jingina ta 2% da ake bukata.

  Sai kajira farashin canjin yahau.

  Idan kasayi dandazo guda daya (rabo 100,000) na GBP/USD akan farashin 1,50000, kana siyan fam 100,000 ne, wanda yakai darajar $150,000 (rabo 100,000 na GBP * 1,50000).

  Since junginar da ake bukata ta 2% ce, sabida haka za’a ajiye dalar Amurka $3,000 a gefe acikin asusunka domin a bude cinikayyar ($150,000 * 2%).

  Yanzu zaka iya kula da fam 100,000 da dalar Amurka $3,000

  Hasashenka yazama ya zama gaskiya kuma kayi ra’ayin ka sayar. Ka rufe matsayarka a 1.50500. zaka iya cin ribar dalar Amurca $500.

image_stage2.1.png
  idan ka yanke shawarar rufe matsaya, za’a dawo maka da ajiyar dakayi ta asali (“jingina”) sannan ayi lissafi na faduwa ko ribar daka samu.

  Wannan riba ko faduwa ita za’a tura asusunka.£

  Bara mu sake nazari akan misalign GBP/USD daya gabata.

  GBP/USD ya tashi da danabunda baifi rabin ……… bama ……….. day aba. Rabi ne kacal.

  Amma kasamu ribar dalar Amurka $500!

  A yayin da gyangyadi mai karfi ya dauke ka!

  Tayaya? Saboda ba cinikayya fan daya £1 kawai kakeyi.

  Idan da ace girman matsayarka £1 ne, to da………..daya kawai zaka samu.

  Amma girman matsayarka £100,000 (ko $150,000) a sand aka bude cinikayyar.

  Abun sha’awar shi ne baka bukatar saika saka gaba daya adadin.

  Abunda kawai aka bukata domin abude cinikayyar shi ne $3,000 a jingina.

  Ribar dalar amurka $500 daga jarin $300 shi ne aka samu 16.67%

  Acikin mintuna ashirin!

  Wannan shi ne karfin jarin aro!

  Dan karamin ajiya ta jingina zata iya kaika kasamu babbar riba haka kuma zata iya kaika kayi babbar asara.

  Kuma yana nufin cewa dan karamin motsi zai iya kaika gwargwadon babban motsi a wajen girman kowacce asara ko riba wanda zai iya taimaka maka ko akasin haka.

  Haka zalika zaka iya yin asarar $500 acikin mituna ashirin.

image_stage2.2.png
  Da baka tashi daga mafarki ba. Da ka fada cikin mafarki!

  Jarin aro mai girma yanada dadin ji (annashuwa), amma kuma zai iya zama mummuna.

  Misali, kabude asusun cinikayyar asuwar canjin kudi da dan karamin adadin kudi na $1,000. Dillalinka ya nuna nufin kayi amfani da jarin aro na kimanin 100:1 ta yadda zaka iya bude matsayar $100,000 EUR/USD.

  Dan karamin kari (100) a tsakanin jerin kudade biyu da kake cinikayya dasu zai mayar da asusunka $0! Dan karamin motsi na 100 daidai yake da €1! Ka tashi asusunka daga aiki da farashin motsi na euro 1 kacal. Muna tayaka murna!

  A yayin da kake cinikayya a jingina, yanada kyau kasan cewa hatsarinka yana damfare da cikakkiyar darajar girman matsayar ka.

  Zaka iya tashin asusunka daka aiki dawuri idan bakasan yadda jingina yake aiki ba. Munaso ka gujewa haka. Saboda wannan hatsari muka sadaukar da sashe guda akan yadda cinikayyar jingina take aiki, ana kiransa da suna cinikayyar jingina ta 101. (Margin Trading 101).

  Juyawa

  A gameda matsayoyin da suke abude a lokacin dakatarwar dillalinka (yawanci 5:00 na yamma ET), akwai “kudin juyawa” na kullum kuma ana kiransa da “kudin musanya” wanda dan kasuwa yake biya ko yake samu, ya dangaanta da matsayoyin daya bari abude.

  Idan bakason kasamu ko ka biya riba akan matsayoyinka, to abu mai sauki shi ne ka tabbatar gaba daya arufe suke kafin karfe 5:00pm ET, lokacin da aka tanada na rufe kasuwar kowace rana.

  Tunda kowanni cinkayyar kudi ta hada da rancen kudi daya domin kasayi wani, ribar kudaden juyawa tana cikin cinikayyar kasuwar canjin kudi.

  Ana biyan riba ne akan kudin da aka aro

  Ana samun riba ne akan kudin da aka siyo.

  Idan kana siyan kudi da farashin riba mai tsada akan wanda kake arowa, to gaba daya bambancin ribar zai zama mai kyau (wato USD/JPY) kuma zaka samu riba a sakamakon haka.

  A daya bangaren kumaa, idan bambancin farashin ribar yazama mara kyau to kai zaka biya.

  Domin Karin bayani akan yadda juyawa take aiki, kaduba shafin mu na Forexpedia wanda yayi bayani akan juyawa

  Kasani cewa dayawa daka cikin dillalan kasuwar canji suna daidaita farashishshikansu na juyawa a karkashin al’amura daban daban (misali asusun kudin aro, farashin aron kudi a tsakanin bankuna).

  Da fatan zaka tuntubi dillalinka domin Karin bayani kan kayyadaddun farashin juyawar su dakuma hanyoyin sakawa da zarewa.

  Wannan taburi ne dazai taimaka wajen gano bambancin farashin riba na manyan kudade.

  Alakar farashin riba

image_stage2.3.png
  Daga baya, zamu koya muku komai gameda yadda zaku iya amfani da bambancin farashin riba yayi fa’ida a gareku.

https://minnews.wikifx.com/How-Do-You-Trade-Forex/2-Know-When-to-Buy-or-Sell-a-Currency-Pair.html
Back to top
Permissions in this forum:
You cannot reply to topics in this forum