Forex.market
Would you like to react to this message? Create an account in a few clicks or log in to continue.

Go down
avatar
Admin
Admin
Posts : 101
Join date : 2021-12-20
https://forex-market.africamotion.net

Wikifx:Menene Pip a Forex? Empty Wikifx:Menene Pip a Forex?

Tue Jan 18, 2022 4:32 am
[size=32]  A wannan gaba, bari muyi dan lissafi, dan kadan kawai.
[size=32]  Watakila kun taba jin labarin “pips”“points““pipettes”, da “lots” a gari, to yanzu zamuyi bayanin su sannan mu nuna yadda ake lissafa darajar su.[/size]
[/size]
Wikifx:Menene Pip a Forex? Stage3
[size]
[size=32]  Bi wannan sakon a nutse domin yanada amfani ga dukkan wasu masu kasuwancin forex.[/size]
[size=32]  Karda kuyi garajen fara kasuwancin sa har sai kun gamsu da darajar Pip tare da yadda lissafin riba da faduwarsa yake.[/size]
[size=42]  Wai menene Pip?[/size]
[size=32]  Mizanin da ake amfani dashi wajen lissafa sauyin daraja tsakanin kudaden kasashe biyu ake kira "Pip"[/size]
[size=32]  Idan EUR/USD ya motsa daga 1.1050 zuwa 1.1051, wannan karin .0001 USD a daraja dai dai yake da PIP DAYA.[/size]
[size=32]  Pip yawancin lokuta shine lamba ta karshe dake zuwa bayan digo a farashin kudin wata kasa.[/size]
[size=32]  Yawancin kudaden musaya biyu ana lissafasu ne har zuwa digo 4, amma banda wasu kamar rukunin su Japanese yen (wanda ake lissafinsu zuwa digo biyu kacal).[/size]
[size=32]  Alal misali, ga duk EUR/USD, lissafinsu shine 0.0001, sannan ga duk USD/JPY,lissafinsu shine 0.01.[/size]
[/size]
Wikifx:Menene Pip a Forex? Stage3.1
[size]
[size=42]  Menene Pipette?[/size]
[size=32]  Wannan sune dillalai masu yiwa kudin kasashe daraja fiye da ainahin digo“4 da 2” zuwa digo “5 da 3”.[/size]
[size=32]  Sune ke dillancin FICTIONAL PIPS,da ake kira“points” ko “pipettes.”[/size]
[size=32]  Idan bayani akan “pip” bai rikirkitar da sabon dan cinikayyar forex ba, to bari muyi karin haske mai zurfi mu nuna cewa “point” ko “pipette” ko “fractional pip”daya dai dai yake da “daya bisa goma na pip“.[/size]
[size=32]  Alal misali, idan GBP/USD ya motsa daga 1.30542  zuwa 1.30543, wannan .00001 USD karin shi ake kira PIPETTE[/size]
[/size]
Wikifx:Menene Pip a Forex? Stage3.2
[size]
[size=32]  Ga bayanin yadda Fractional pips suke a jadawalin saye da siyarwa.[/size]
[/size]
Wikifx:Menene Pip a Forex? Stage3.3
[size]
[size=32]  A jadawalin saye da sayarwar, lambar dake wakiltar daya bisa goma na pip kusan kodayaushe tana bayyana ne a bangaren daman lambobi biyu masu manyan rubutu.[/size]
[size=32]  Wannan shine“taswirar” pip wanda zai taimaka wajen karantar pips…[/size]
[/size]
Wikifx:Menene Pip a Forex? Stage3.4
[size]
[size=42]  Yanda ake lissafa darajar Pipk[/size]
[size=32]  Kamar yanda kowane kudin kasa yake da irin nashi kimar, ya zama dole a lissafa darajar pip dai-dai da farshin wannan kudi.[/size]
[size=32]  A misalan da zasu biyo baya zamu yi amfani da mizanin digo 4 wajen yiwa kudi daraja.[/size]
[size=32]  Domin fuskantar yanda lissafin yake , mizanin musayar kudin zai kasance kamar haka. ( EUR/USD a farashin 1.2500 zai zama an rubuta shi a matsayin“1 EUR / 1.2500 USD”)[/size]
[size=32]  MISALI #1: USD/CAD = 1.0200[/size]
[size=32]  Za a karanta shi a matsayin 1 USD dai dai yake da 1.0200 CAD (ko kuma 1 USD/1.0200 CAD)[/size]
[size=32]  (sauyin daraja na kudin wata kasa) sau adadin mizanin musayar kudi = darajar pip ( a mizanin kudin kasa ta asali)[/size]
[size=32]  [.0001 CAD] x [1 USD/1.0200 CAD[/size]
[size=32]  Ko kuma kawai:[/size]
[size=32]  [(.0001 CAD) / (1.0200 CAD)] x 1 USD = 0.00009804 USD ga duk kwaya daya da aka yi dillancin sa.[/size]
[size=32]  Yin duba ga wannan sassaukan lissafi, idan muka yi dillancin USD/CAD kwaya 10,000 , to pip daya tal zai sauya daraja zuwa kimanin 0.98 USD (10,000 units x 0.00009804 USD/unit).[/size]
[size=32]  Mun ce“kimani” saboda yayin da mizanin musayar kudin ya sauya, itama darajar kowane pip kwaya daya takan sauya.[/size]
[size=32]  MISALI #2: GBP/JPY = 123.00[/size]
[size=32]  Nan ma wani misalin ne inda akayi amfani da kudin wata kasa tare da Japanese Yen a matsayin kudin kasa na asali.[/size]
[size=32]  Mu kula cewa a wannan gamin kudi za'ayi amfani da digo biyu kacal wajen awon sauyin darajar na 1 pip (yawancin kudade suna amfani da digo hudu ne). A irin wannan yanayi, sauyin pip 1 zai zamo .01 JPY.[/size]
[size=32]  (sauyin daraja na kudin wata kasa) sau adadin mizanin musayar kudi = darajar pip ( a mizanin kudin kasa ta asali)[/size]
[size=32]  [.01 JPY] x [1 GBP/123.00 JPY][/size]
[size=32]  Ko kuma kawai:[/size]
[size=32]  [(.01 JPY) / (123.00 JPY)] x 1 GBP = 0.0000813 GBP[/size]
[size=32]  A don haka, duk sanda zamuyi dillancin GBP/JPY kwaya 10,000, kowane sauyin daraja na pip ya doshi kimanin 0.813 GBP.[/size]
[size=42]  Yanda ake Gane Darajar Pip ta kudin da ake amfani dasu a Asusun ka na Trading Account.[/size]
[size=32]  Tambaya ta karshe a yayin gano darajar pip dai-dai da aljihun ka itace, “Menene darajar pip a kudin da ake amfani dasu a Asusu na na Trading Account?”[/size]
[size=32]  Tunda ai, ita wannan harkalla a kasuwar duniya ake yin ta, kuma ba kowa ne yake da asusu mai amfani da kudin kasa iri daya jal ba.[/size]
[size=32]  Hakan yana nufin darajar pip ana kididdiga ta ne dai-dai da darajar irin kudin da asusun mutum yake harkalla da su.[/size]
[size=32]  Wannan lissafin watakila shi yafi ko wanne sauki; a saukake: “darajar pip din da ka gano” Sau/a kasafta shi da mizanin musayar kudi na asusun ka, da kuma kudin da zaka yi kasuwancin su.[/size]
[size=32]  Idan kudin“darajar pip din da ka gano” irin na kasa daya ne da kudin kasa ta asali a jadawalin musayar kudi:[/size]
[size=32]  Yin amfani da misali daya gabata na GBP/JPY, bari mu sauya darajar pip da aka gano na .813 GBP zuwa darajar pip a kudin USD ta haryar amfani da kuma GBP/USD din 1.5590 a matsayin mizanin musayar mu.[/size]
[size=32]  Idan kudin da zamuyi musaya kuma sun bambamta da kudin kasa ta asali a mizanin musayar, abin da kawai zamuyi shine; zamu kasafta“darajar pip din da ka gano”da mizanin musayar mu:[/size]
[size=32]  .813 GBP ga duk pip daya / (1 GBP/1.5590 USD)[/size]
[size=32]  Ko[/size]
[size=32]  [(.813 GBP) / (1 GBP)] x (1.5590 USD) = 1.2674 USD ga duk sauyi daya na pip.[/size]
[size=32]  Don haka, ga duk .01 sauyin pip a GBP/JPY, darajar kowane daya a kwaya 10,000 zai sauya da kimanin 1.27 USD.[/size]
[size=32]  Idan kudin da zamuyi musaya kuma iri daya ne da kudin kasa ta asali a mizanin musayar kudi, to sai muce,“darajar pip din da ka gano”sau mizanin musayar kudin kasar asali.[/size]
[size=32]  Yin amfani da misalin USD/CAD daya gabata, muna son mu gane darajar pip din .98 USD a New Zealand Dollars. Zamuyi amfani da .7900 a matsayin mizanin musayar kudin mu:[/size]
[size=32]  0.98 USD ga kowanne pip X (1 NZD/.7900 USD)[/size]
[size=32]  Ko[/size]
[size=32]  [(0.98 USD) / (.7900 USD)] x (1 NZD) = 1.2405 NZD ga kowane sauyi a pip[/size]
[size=32]  Ga kowane motsawa na .0001 pip a USD/CAD daga misalin mu da ya gabata, kowane daya a cikin 10,000 ya sauya daraja da kimanin 1.24 NZD.[/size]
[size=32]  Duk da kasancewar ka/ki gwaska a lissafi – akalla lissafin darajar pip–watakila yanzu haka kana/kina wuri-wuri da idanu kana/kina tunanin, “To wai da kaina zan ringa yin wannan dogon lissafin a duk sanda hanyi harkallar pip?”[/size]
[size=32]  To dai, amsar itace A'A da manyan baki.. Kusan dukkanin lissafin dillalan forex ne zasuyi lissafin kai tsaye, amma yana da fa'ida idan har ka/kika gane haryar da suke bi su yi lissafin.[/size]
[size=32]  Idan kuma har ya kasance dillalin ka/ki bai yi lissafin ba, babu damuwa! Zaku iya amfani da Pip Value Calculator din mu! Ko bamu kayatar da ku bane?![/size]
[size=32]  A darasi na gaba, zamuyi bayanin yadda wadannan yan kudaden da kamar ba wasu na kirki ba suke zama makudai.[/size][/size]
https://minnews.wikifx.com/How-Do-You-Trade-Forex/3-What-is-a-Pip-in-Forex.html
Back to top
Permissions in this forum:
You cannot reply to topics in this forum